Najeriya-Coronavirus

Sama da mutane 450 sun warke daga cutar corona a Najeriya

Sabuwar cibiyar kula da masu cutar coronavirus dake filin wasa na Mobolaji Johnson Arena a jihar Legas dake Najeriya. 27/3/2020.
Sabuwar cibiyar kula da masu cutar coronavirus dake filin wasa na Mobolaji Johnson Arena a jihar Legas dake Najeriya. 27/3/2020. REUTERS/Temilade Adelaja

Adadin mutanen da cutar COVID-19 ta kama a Najeriya ya kusa kaiwa dubu 3, sakamakon samun karin sabbin mutane 148 dake dauke da cutar a Jihohi 17.

Talla

Alkaluman da hukumar yaki da cututtuka da ke Najeriya suka gabatar sun nuna cewa daga cikin mutane 148 da aka samu dauke da cutar a jiya 43 na Jihar Lagos ne, sai 32 a Kano, 14 a Zamfara, 10 a Abuja, 9 a Katsina, 7-7 a Jihohin Taraba da Barno, 6 a Ogun, 5 a Oyo.

Jihohin bauchi da Edo na da sabbin mutane 3-3, Adamawa da Gombe na da bibiyu, sai Plateau da Sokoto da Kebbi dake da guda-guda.

Bayan gwajin da aka yiwa mutane 19,512 a Najeriya, Lagos ke sahun gaba da mutane 1,226 dake dauke da cutar coronvirus, sai Kano mai mutane 397, Abuja na da 307, Barno 106, Gombe 98, Katsina 92, Ogun 91, Kaduna 84, Bauchi 83, Sokoto 67, Edo 65, Oyo 44, Jigawa 39, Osun 37.

Sauran jihohin sun nuna cewar Zamfara na da mutane 27, Delta 17, Akwa Ibom 16, Kwara16, Taraba 15, Rivers 14, Adamawa 14, Yobe 13, Ondo 13, Kebbi 13, Ekiti 12, Nasarawa 11, Enugu 8, Bayelsa 5, Ebonyi 5, Plateau 4, Niger 4, Benue 2, Imo 2, Abia 2, Anambra guda.

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya tace ya zuwa yanzu, jumillar mutane dubu 2 da 950 suka kamu da cutar coronavirus a kasar, 481 daga cikinsu sun warke, yayin da 98 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.