Coronavirus-Kano

Coronavirus ta halaka karin mutane 5 a Kano

Cibiyar killace masu dauke da cutar coronavirus dake filin wasa na Sani Abacha dake Kano, bayan kammala gininta, 7/4/2020.
Cibiyar killace masu dauke da cutar coronavirus dake filin wasa na Sani Abacha dake Kano, bayan kammala gininta, 7/4/2020. Minu Abubakar/AFP via Getty Images

Ma’aikatar lafiyar Kano ta sanar da mutuwar karin mutane biyar da suka kamu da cutar coronavirus a jihar, yayinda kuma aka sallami karin mutane 3 da suka warke daga cutar.

Talla

A daren ranar laraba hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta sanar da mutuwar mutane 5 a dalilin annobar ba tare da bayyana jihar da suka mutu ba.

Cikin sanarwar da ta fitar da safiyar yau alhamis, ma’aikatar lafiyar Kano ta ce ya zuwa yanzu, jimillar mutane 427 ne suka kamu da cutar coronavirus a jihar, 13 daga cikinsu sun mutu, yayinda 6 suka warke.

Sai dai a nata bangare, kungiyar ma’aikatan jinya na Nas a turance da kuma Ungozoma ta Najeriya reshen Kano, tace yanzu haka ‘ya’yanta 18 ne gwaji ya tabbatar sun kamu da cutar ta coronavirus.

Kafin sanarwar kungiyar ma’aikatan jinyar, kungiyar likitocin Najeriya ce reshen jihar ta Kano, ta bayyana kamuwar likitoci akalla 34 ad cutar ta coronavirus ko COVID-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.