Bakonmu a Yau

Dakta Abubakar Nagoma kan likitoci 34 da suka kamu da cutar corona a Kano

Sauti 03:28
Daya daga cikin kayayyakin asibiti da ake amfani da su wajen gwajin cutar coronavirus.
Daya daga cikin kayayyakin asibiti da ake amfani da su wajen gwajin cutar coronavirus. REUTERS/Dado Ruvic

Kungiyar Likitocin Najeriya reshen jihar Kano yace ya zuwa yanzu likitoci 34 suka harbu da cutar coronavirus a Jihar a kokarin da suke na ceto rayukan jama’a kuma guda daga cikin su ya mutu.Shugaban kungiyar Sanusi Bala ya bayyana haka, inda yake cewa akasarin likitocin sun fito ne daga Asibitin Koyar Malam Aminu Kano da kuma wasu masu zaman kan su.Dr Abubakar Nagoma, shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa a Asibitin Malam Aminu Kano ya yiwa wakilinmu Abubakar Isa Dandago bayani kan wannan asara.