Najeriya-Coronavirus

Adadin masu coronavirus a Najeriya ya haura 3,500

Wani ma'aikacin lafiya yayin taimakawa abokin aikinsa sanya kayan samun kariya daga kamuwa da cutar coronavirus, kafin soma yiwa mutane gwaji a Abuja babban birnin Najeriya. 15/4/2020.
Wani ma'aikacin lafiya yayin taimakawa abokin aikinsa sanya kayan samun kariya daga kamuwa da cutar coronavirus, kafin soma yiwa mutane gwaji a Abuja babban birnin Najeriya. 15/4/2020. REUTERS/Afolabi Sotunde

Hukumomin Najeriya sun ce adadin mutanen da suka harbu da cutar COVID-19 a jiya alhamis sun kai 381 adadi mafi girma da aka taba gani tun bayan barkewar cutar, abinda ya kawo adadin kasar zuwa 3,526, 601 sun warke, 107 kuma sun mutu.

Talla

Adadin da hukumar yaki da cututtuka a Najeriya ta bayar daren jiya sun nuna cewar an samu mutane 381 da suka kamu da cutar a Jihohi 18, abinda ya kawo yawan wadanda suka harbu da cutar a Najeriya zuwa 3,526.

Sabbin alkaluman sun nuna Lagos na da mutane 183, Kano 55, Jigawa 44, Zamfara da Bauchi 19-19, Katsina 11, Borno 9, kwara 8, Kaduna 7, Gombe 6, Ogun 5, Sokoto 4, Oyo da Rivers 3-3, Niger 2, sannan jihohin Akwa Ibom da Enugu da Plateau ke da guda-guda.

Har yanzu Lagos ke sahun gaba wajen samun wadanda suka harbu da cutar inda yawan su ya kai 1,491, sai Kano mai 482, sai Abuja 316, Barno 125, Gombe 109, Katsina 106, Bauchi 102, Ogun 100, Kaduna 90, Sokoto 89, Jigawa 83, sai kuma Edo da Zamfara 65-65.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.