Najeriya-Jigawa

Almajirai 16 da aka maida Jigawa daga Kano na dauke da coronavirus

Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2017 ya nuna cewar, akwai kananan yara miliyan 3 dake bara a jihar Kano.
Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2017 ya nuna cewar, akwai kananan yara miliyan 3 dake bara a jihar Kano. AFP/AMINU ABUBAKAR

Gwamnatin Jihar Jigawa dake Najeriya ta sanar da samun almajirai 16 dake dauke da cutar coronavirus daga cikin 607 da aka yiwa gwaji bayan mayar da su gida daga Kano.

Talla

Kwamishinan lafiyar Jihar Abba Zakari yace Jihar ta tura samfurin gwajin almajiran 607 da aka mayar da su Jigawan daga jihohi da dama, amma sakamakon 45 kawai suka samu, wanda ya nuna cewar 16 da suka fito daga Kano sun harbu.

Kwamishinan yace za a tura wadanda aka tababtar basa dauke da cutar zuwa gidajen iyayensu kuma kowanne daga ciki zai karbi naira dubu 10,000 da kuma tufafi.

Abba Zakari yace sun jiran isowar sakamakon gwajin sauran almajiran, wadanda kuma suka kamu da cutar coronavirus za a killace su a cibiyar kula da wadanda annobar ta shafa a jihar.

Kwamishinan lafiyar na Jigawa ya kuma yi karin bayanin cewar, gwamnati na dakon isowar wasu karin almajiran akalla 99 ‘yan asalin jihar daga jihar Filato, wadanda za a killace su tsawon mako 2, don tabbatar da cewa basa dauke da cutar coronavirus.

Zuwa yanzu alkalumman da gwamnatin Jigawa ta fitar sun nuna cewa jumillar almajirai subu 1 da 114 ‘yan asalin jihar aka maida gida daga jihohin Kano, Kaduna, Gombe da kuma Nasarawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.