Najeriya-Amurka

An bankado karin makudan kudaden marigayi Abacha a Turai

Tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha, daga tsakiya yayin bikin kaddamar da gidauniyar samar da zaman lafiya da hadin kan kasa a birnin Abuja. 17 ga Nuwamba, 1997.
Tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha, daga tsakiya yayin bikin kaddamar da gidauniyar samar da zaman lafiya da hadin kan kasa a birnin Abuja. 17 ga Nuwamba, 1997. Stringer/Reuters

Gwamnatin Amurka ta sanar da gano wasu sabbin makudan kudade na dala miliyan 319, kwatankwacin naira biliyan 121, da Amurkan tace tsohon shugaban Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha ya boye a kasashen Birtaniya da kuma Faransa.

Talla

Cikin sanarwar da ya fitar, ofishin jakadancin Amurka a Najeriya yace dala miliyan 167 na boye a Faransa, yayinda dala miliyan 152 ke Birtaniya.

Gano sabbin kudaden ya zo ne kasa da mako guda bayanda Amurka ta mikawa Najeriya dala miliyan 311 da ake tuhumar tsohon shugaban Najeriyar marigayi Janar Sani Abacha da boyewa a wani bankinta.

Gwamnatin Najeriya ta kwashe tsawon shekaru tana fafutukar karbo kashin farko na dala miliyan 311 daga Amurka, da ake zargin tsohon shugabanta a zamanin mulkin soja ya boye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.