Najeriya

Kotun Koli ta soke daurin shekaru 12 da aka yankewa tsohon Gwamnan Abia

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu.
Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu. YouTube

Kotun Kolin Najeriya ta soke hukuncin daurin shekaru 12 da babbar kotun kasar dake Legas ta tabbatar kan tsohon gwamnan Jihar Abia Orji Uzor Kalu, bisa samunsa da laifin cin hanci da rashawa.

Talla

Kotun Kolin ta kuma soke hukuncin daurin da aka yankewa daraktan kula da fidda kudade da asusun fadar gwamnatin jihar ta Abia Ude Udeogu, a zamanin mulkin tsohon gwamnan Uzor Kalu.

Idan za a iya tunawa, ranar 5 ga watan Disambar shekarar 2019, mai Shari’a Mohammed Idris na babbar kotun Najeriya dake Legas, ya yanke hukuncin daurin kan tsohon gwamnan jihar ta Abia, tsawon shekaru 12, saboda samunsa da laifin sace dukiyar al’umma, yayinda shi kuma na hannun damansa mista Udeogu, mai shari’a Idris ya daure shi tsawon shekaru 10.

Bangare na uku da aka gurfanar gaban kotun a waccan lokacin shi ne kamfanin ‘Slok Nigeria Limited’ mallakin tsohon gwamnan na Abia, wanda kotun ta bada umarnin kwace kadarorinsa a mikawa gwamnatin Najeriya, bayan samun kamfanin da laifin yiwa gwamnatin zamba cikin aminci.

Tun da farko dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ce ta gurfanar da tsohon Gwamna Orji Uzor Kalu, bisa tuhumarsa da karkatar da naira biliyan 7 da miliyan 65 daga aljihun gwamnatinsa.

Sai dai bayan yanke musu hukuncin, da kuma rashin gamsuwa da shi, tsohon Gwamnan tare da na hannun damansa mista Udeogu suka shigar da kara gaban Kotun Kolin Najeriya, wanda kuma a yau Juma’a tawagar Alkalai 7 suka yanke hukuncin soke daurin da aka yi musu, tare da bada umarnin sake sauraron shari’ar.

Tuni dai hukumar EFCC ta bayyana aniyar sake gurfanar da Orji Uzor Kalu gaban kotu, domin tabbatar da laifin da take tuhumarsa da aikatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.