Najeriya-Lagos

Mai yiwuwa yawan masu cutar corona a Legas ya kai dubu 120 - Gwamnati

Wani sashi na birnin Legas dake kudancin Najeriya, yayin hada hadar kasuwanci. 23/12/2016.
Wani sashi na birnin Legas dake kudancin Najeriya, yayin hada hadar kasuwanci. 23/12/2016. Reuters / Akintunde Akinleye

Gwamnatin Legas a Najeriya tace mai yiwuwa yawan wadanda za su kamu da cutar coronavirus a jihar ya kai dubu 120, idan annobar ta kai kololuwa a tsakanin watan Yuli da Agusta.

Talla

Kwamishinan lafiyar jihar dakta Akin Abayomi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a yau Juma’a.

Sai dai kwamishinan yace an kafa ginshikin wannan kididdiga ce bisa yanayin yadda ake samun karuwar wadanda suke kamuwa da cutar cikin jihar a baya bayan nan, amma hakan baya nufin babu makawa sai hasashen ya tabbata.

Dakta Abayomi ya bada misalin cewar wata guda da ya gabata ranar 7 ga watan Afrilu, mutane 10 kawai ko sama da haka kadan ake samu sun kamu da cutar coronavirus duk rana a jihar, amma bayan mako biyu, adadin ya kai 32 duk rana, daga bisani kuma ya kai 72 tare da zarce hakan, hauhawar da kwararru suka yi hasashen cewa za ta cigaba har zuwa lokacin da annobar za ta kai kololuwar karfi a jihar, daga baya kuma kaifinta ya ragu.

Yanzu hakada dai jumillar mutane dubu 3 da 526 suka kamu da coronavirus a Najeriya, 601 sun warke, 107 kuma sun mutu.

Daga cikin wadanda suka kamun, Lagos ke sahun gaba da mutane dubu 1 da 491, sai Kano mai 482, sai Abuja 316, Barno 125, Gombe 109, Katsina 106, Bauchi 102, Ogun 100, Kaduna 90, Sokoto 89, Jigawa 83, sai kuma Edo da Zamfara 65-65.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.