Najeriya

Masu coronavirus sun sake yin zanga-zanga a Gombe

Misalin fasalin kwayar cutar Coronavirus da aka yi amfani da Komfuta wajen fitarwa.
Misalin fasalin kwayar cutar Coronavirus da aka yi amfani da Komfuta wajen fitarwa. MAURIZIO DE ANGELIS/SCIENCE PHOTO LIBRARY

Masu dauke da cutar coronavirus a Gombe sun gudanar da sabuwar zanga-zanga, kwanaki 3 bayan gudanar da makamanciyarta a ranar talatar da ta gabata a Kwadon.

Talla

A farkon makon nan 5 ga watan Mayu, wasu masu cutar coronavirus dake asibitin koyarwa na garin Gombe da wasunsu dake cibiyar killace wadanda suka kamu da cutar a karamar hukumar Yamaltu Deba, suka datse babbar hanyar dake ratsa yankin har tsawon akalla mintuna 30 suna zanga-zanga, kan rashin samun kulawar jami’an lafiya, inda wani gungu na jama’ar gari masu lafiya suka mara musu baya, abinda ya kai ga sai da jami’an tsaro suka shiga lamarin.

Sai dai ‘TheCable’ daya daga cikin jaridun Najeriya da suka dauki labarin, sun ruwaito cewar wasu daga cikin marasa lafiyar basu koma inda aka killace su ba, dalilin arcewar da suka yi.

Rahotanni sunce bayan zanga-zangar ranar talata an baiwa marasa lafiyar dake cibiyar killace masu coronavirus kulawa sosai, to jin labarin hakan yasa masu cutar dake asibitin koyarwa kukewa kan bafa za su yarda a maida su saniyar ware ba, mafarin zanga-zangar sabuwa ta yau kenan.

Kawo yanzu jami’an tsaro sun daidata lamurra.

Alkalumman hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC sun nuna cewa Jumillar mutane 109 ne suka kamu da cutar coronavirus a Gombe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.