Najeriya-Lagos

Mutane da dama sun tsere bayan gwaji ya tabbatar suna da cutar corona

Sabuwar cibiyar killacewa tare da kula da masu cutar coronavirus dake tsohon filin wasa na Onikan a birnin Legas, dake Najeriya. 27/3/2020.
Sabuwar cibiyar killacewa tare da kula da masu cutar coronavirus dake tsohon filin wasa na Onikan a birnin Legas, dake Najeriya. 27/3/2020. REUTERS/Temilade Adelaja

Gwamnatin Legas dake Najeriya tace akwai mutane da dama a Jihar da aka gano suna dauke da cutar coronavirus, amma sun gudu saboda kada a kaisu inda ake killace mutane domin kula da lafiyarsu.

Talla

Kwamishinan kula da lafiyar jihar Akin Abayomi ya sanar da haka, inda yake cewa wannan na daga cikin dalilin da ya sa har yanzu gadajen da aka ware domin aje masu fama da cutar basu cika ba, duk da yake Jihar ce ke sahun gaba wajen yawan masu dauke da cutar.

Abayomi yace sau tari idan an gwada mutane an tabbatar suna dauke da cutar, lokacin da aka je dauko su domin kai su inda za’a kula da lafiyar su, sai a tarar sun gudu.

Kwamishinan yace fatar su itace wadanda aka gano suna dauke da cutar da su bada hadin kai domin kare lafiyar su, inda yake cewa Jihar bata lokacin farautar irin wadannan mutane alhali akwai wadanda suka suke bukatar ganin an kula da su.

Abayomi yace sun inganta wuraren da suke aje masu fama da cutar sabanin yadda aka yi lokacin annobar Ebola, kuma har an kwantar da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin da suka harbu da cutar a wurin.

A karshe kwamishinan ya bukaci mazauna Lagos da su kwantar da hankalin su, domin gwamnatin na daukar matakan da suka dace wajen ganin ta dakile cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.