Najeriya

Annobar coronavirus ta soma halaka 'Yan Jarida a Najeriya

Wasu ma'aikatan gidan talabijin na Najeriya NTA, yayin gudanar da aiki.
Wasu ma'aikatan gidan talabijin na Najeriya NTA, yayin gudanar da aiki. REUTERS/Akintunde Akinleye

Kungiyar ‘Yan Jaridu a Najeriya ta koka kan halin da ‘ya’yanta ke ciki yayin gudanar da ayyukansu a daidai lokacinda ake fama da annobar coronavirus da ta addabi duniya.

Talla

Kungiyar ‘Yan Jaridun tace suna fuskantar makamancin hadarin da likitoci da sauran ma’aikatan jinya ke ciki na kamuwa da cutar ta coronavirus, inda tace tuni wasu ‘Yan Jaridu 3 suka rasa rayukansu sakamakon harbuwa da annobar, yayinda wasu da dama suka kamu.

Wakilinmu daga Abuja Muhammadu kabiru Yusuf ya hada mana rahoto kan halin da ake ciki.

Annobar coronavirus ta soma halaka 'Yan Jarida a Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.