Majalisar Dinkin Duniya

Duniya ta cika shekaru 40 da samun nasara kan cutar Kyanda

Wani karamin yaro dan kasar Sudan ta Kudu, yayin karbar allurar rigakafin cutar Kyanda a Juba, babban birnin kasar. 4 ga Fabarairu shekarar 2020.
Wani karamin yaro dan kasar Sudan ta Kudu, yayin karbar allurar rigakafin cutar Kyanda a Juba, babban birnin kasar. 4 ga Fabarairu shekarar 2020. REUTERS/Samir Bol/File Photo

Yau ake cika shekaru 40 da yadda duniya ta samu nasarar yaki da cutar kyanda wadda ta kwashe shekaru sama da 3,000 ta kuma kashe mutane sama da miliyan 300 a fadin duniya.

Talla

Yunkurin Majalisar Dinkin Duniya da dubban jami’an kula da lafiya a kasashen duniya ya taimaka wajen kwashe shekaru 10 ana yiwa mutane sama da miliyan 500 allurar rigakafi kamun samun nasara akan cutar.

Hukumar lafiya ta Duniya tace an kashe kudin da ya kai Dala miliyan 300 wajen gudanar da rigakafin abinda ya taimaka wajen kawar da cutar da kuma kare duniya asarar Dala biliyan guda kowacce shekara tun daga shekarar 1980.

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus yace yayin da duniya ke fama da wannan annoba ta COVID-19, nasarar da Bil Adama ya samu kan cutar kyanda wata manuniya ce cewar ana iya samun nasara yanzu muddin kasashen duniya suka hada kan su.

Gebreyesus yace hadin kan kasashen duniya da gudumawar kimiya wajen samar da maganin rigakafi sun taimaka gaya wajen magance cutar kyanda a duniya.

Jami’in yace wancan nasarar ta bada damar wajen shawo kan wasu cututtuka na daban cikin su harda polio wanda yanzu haka ta takaita zuwa kasashe biyu kacal a duniya, yayin da kasashen duniya 187 suka kawar da cutar kurkunu daga cikin su, inda yanzu haka cutar ta takaita ce a kasashe 7 kacal.

Shugaban hukumar lafiyar yace haka kuma an samu nasarar kawar da cutar zazzabin cizon sauro a kasashe 38 na duniya, yayin da kasashe 57 suka shawo kan cutar tarin fuka.

Gebreyesus ya gabatar da kan sarki na musamman da akayi domin karrama kasashen duniya da ma’aikatan lafiyar da suka bada gudumawa wajen samun wadannan nasarori.

Kasashe irin su Guinea da India da Najeriya da Philippines da kuma Togo sun kaddamar da irin wadannan kan sarki dake goyan bayan shirin yaki da cutar kyanda da kuma nasarar da aka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.