Najeriya-Borno

Gwamnatin Borno za ta tattara bayanan Almajirai a maimakon maida su gida

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum.
Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum. RFI Hausa / Ahmad Abba

Gwamnatin Borno tace har yanzu babu almajirin da ta maida zuwa garinsa ko kuma ta karba daga wata jiha, a daidai lokacinda gwamnatocin jihohi a arewacin Najeriya suka dukufa wajen musayar almajiran dake yankunansu ta hanyar maida su asalin inda suka fito.

Talla

Yayin ganawa da manema labarai a Maiduguri cikin karshen makon nan, mataimakin gwamnan jihar Borno Alhaji Umar Kadafur yace a maimakon, kwasar almajiran gami da maida su zuwa garuruwansu na ainahi, Gwamnati za ta tattara bayanai ne na yaran da malamansu dake daukacin tsangayun karatun Allon dake jihar ta Borno, domin tsara matakai na gaba.

Kadafur yace kamata yayi hukumomi su rika fahimtar yanayin mawuyacin halin da almajirai ke ciki gami da tausaya musu, domin hakan zai taimaka wajen yin taka-tsantsan kan batun daukar matakan warware matsalar almajiranci musamman a lokacin da duniya ke fuskantar annobar coronavirus.

Mataimakin Gwamnan na Borno ya jaddada cewar, almajirai musamman kananan yara daga cikinsu na bukatar tausayawa da kulawa, la’akari da cewar ba su ne suka kirkiri tsari ko yanayin da suka tsinci kansu a ciki ba.

A baya bayan gwamnonin jihohin Najeriya a arewacin kasar suka yi ta musayar maida almajirai zuwa garuruwansu, shirin da bulllar annobar COVID-19 ta karfafa, wanda wasunsu suka ce dama sun tsara aiwatarwa don kawo karshen tsarin karatun almajiranci, matakin da zai magance matsalar barace-barace da kananan yara ke yi akan tituna da layukan unguwanni, ba tare da samun kulawa ta bangaren lafiya da ilimin karatun boko ba.

Tuni dai Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, gwamnatinsa tayi nasarar mayar da almajirai sama da dubu 30 zuwa jihohin da suka fito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.