Najeriya-Kano

Karin mutane 16 sun warke daga cutar coronavirus a Kano

Cibiyar killace masu cutar coronavirus dake Kwanar Dawaki, a Jihar Kano.
Cibiyar killace masu cutar coronavirus dake Kwanar Dawaki, a Jihar Kano. RFI Hausa / Abubakar Dangambo

Gwamnatin Kano ta sanar da sallamar karin mutane 16 daga cibiyoyin killace masu fama da coronavirus, bayanda gwaji har kashi biyu ya tabbatar da cewa sun warke daga cutar.

Talla

Cikin sanarwar da ya rabawa manema labarai cikin karshen makon nan a garin Kano, kwamishin yada labaran jihar Muhammad Garba yace karin wadanda aka sallamar ya kai jumillar adadin wadanda suka warke daga annobar coronavirus a Kano kaiwa 22.

Bayanai sunce cikin karin mutanen da aka sallama akwai kwamishinan lafiyar Kanon dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa da kuma mataimakin shugaban kwamitin yakar cutar corona a Jihar Farfesa Abdulrazak Garba Habeeb.

Alkalumman hukumomin lafiya sun nuna cewar, zuwa lokacin wallafa wanna labari jumillar mutane 547 suka kamu da coronavirus a Kano, 22 daga ciki sun warke, yayinda 18 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.