Najeriya-Kano

Marasa lafiya sun yi garkuwa da likitoci a cibiyar killace masu COVID-19

Cibiyar killace masu cutar coronavirus dake Kwanar Dawaki, Jihar Kano.
Cibiyar killace masu cutar coronavirus dake Kwanar Dawaki, Jihar Kano. RFI Hausa / Abubakar Dangambo

Rahotanni daga Kano a Najeriya sun ce mutanen da aka killace su a cibiyar kula da masu cutar coronavirus ko COVID-19 dake Kwanar Dawaki, sun yi garkuwa da likitoci 2 da ma’aikaciyar jinya guda.

Talla

Bayanai sun ce likitocin sun ga takansu ne a daidai lokacin da suke kan aikin duba mutanen da aka killace, wadanda suka yi amfani da damar wajen garkame jami’an lafiyar a daya daga cikin dakunan kwantar da marasa lafiya.

Majiya daga cibiyar killace masu cutar ta corona a Kwanar Dawakin tace, marasa lafiyar sun fusata ne saboda shafe mako guda a killace, ba tare da sanin matsayinsu ba, kan ko suna dauke da cutar ko kuma basa dauke da ita, duk da cewar an yi musu gwaji.

Yayin tabbatar da gaskiyar labarin shugaban kungiyar likitoci ta Najeriya reshen Kano, Farfesa Aminu Mohammed, yace sai da aka kaiwa likitocin da ma’aikaciyar jinyar daukin gaggawa ta hanyar karya kofar dakin da suke kulle, sakamakon tsananin zafin da ya addabe su.

A baya bayan nan ne dai masu dauke da cutar coronavirus a Gombe suka gudanar da zanga-zanga har kashi biyu a Kwadon, bayan da suka fusata da abinda suka kira yin watsi da su a cibiyoyin da suke killace, ba tare da basu kulawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.