Najeriya-Coronavirus

Najeriya ta samu karin masu corona 386, adadi mafi girma a rana 1

Wani jami'in lafiyar Najeriya yayin yiwa wata mata gwajin cutar coronavirus a Abuja.
Wani jami'in lafiyar Najeriya yayin yiwa wata mata gwajin cutar coronavirus a Abuja. Kola Sulaimon/AFP via Getty Images

Najeriya ta samu karin mutane 386 da suka kamu da cutar coronavirus a ranar guda, adadi mafi girma da kasar ta gani tun bayan bullar annobar cikinta, a watan Fabarairun da ya gabata.

Talla

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC tace zuwa yanzu jumillar mutane dubu 3 da 912 suka kamu da cutar a Najeriya, daga cikinsu 679 sun warke, yayinda annobar ta halaka wasu 117.

Hukumar NCDC tace an sabbin mutanen 386 da suka kamu ne a jihohin Najeriya 20, inda a Legas kadai aka samu karin masu cutar ta coronavirus guda 176, Kano 65, Katsina 31, Abuja 20, 17 a Borno, Bauchi na da sabbin mutane 15 da suka kamu da corona, yayinda Nasarawa ta samu karin 14, sai Ogun mai 13, da Filato mai karin mutane 10 da annobar ta harba.

A sauran jihohin da aka samu karin mutanen da coronavirus ta kama, Oyo da Rivers da kuma Sokoto na da mutane 4-4 kowannensu, sai Kaduna mai mutane 3, Edo da Ebonyi 2-2, sai kuma jihohinImo, Osun da kuma Gombe masu mutane 1-1.

Har yanzu Legas ke jan ragamar zama inda cutar tafi yaduwa, bayan samun jumillar wadanda cutar coronavirus din ta kama dubu 1 da 226, sai Kano mai mutane 547, Abuja 336, sai Borno mai 147, Gombe 110, sai Katsina 137, Bauchi 117, Kaduna 93, Ogun 113 sai Sokoto da JIgawa masu 94 da kuma 83.

A sauran jihohin Edo na da jumillar mutane 68, a Zamfara 65, Oyo 59, Osun 38, Kwara 28 sai Kebbi da mutane 18. Sauran sun hada da, Akwa Ibom da Delta na mutane 17-17, a Taraba da Adamawa da Ondo da Filato, jumillar mutane 15-15 suka kamu ta cutar coronavirus a jihohin, Rivers na da 21, a Yobe mutane 13, Ekiti 12, Nasarawa 11, sai Enugu dake da mutane 10, Niger 9, Bayelsa 5, sai Ebonyi mai mutane 7, mutane 2-2 suka kamu a Abia da benue, sai Imo mai mutane 3, yayinda a Anambra har yanzu mutum daya ya kamu.

Kawo yanzu mutane dubu 23, da 835 hukumomin lafiya a Najeriya suka yiwa gwajin cutar coronavirus tun bayan bullar annobar cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.