Kano

Allah ya yiwa Dan Iyan Kano rasuwa

Dan Iyan Kano, Hakimin Dawakin, marigayi Alhaji Yusuf Bayero.
Dan Iyan Kano, Hakimin Dawakin, marigayi Alhaji Yusuf Bayero. PM News

Allah ya yiwa Dan Iyan Kano kuma Hakimin Dawakin Kudu Alhaji Yusuf Bayero rasuwa.

Talla

Labarin mutuwar Dan Iyan na Kano ya bayyana ne da safiyar yau Lahadi, kamar yadda jaridar The Nation dake Najeriya ta ruwaito.

An haifi marigayi Yusuf Bayero a shekarar 1933 a Kano, inda yayi karatun Islama da na Boko.

Marigayin ya taba zama dan majalisar lardin Arewacin Najeriya inda har ya rike mukamin sakataren majaliar.

Bayan juyin mulkin shekarar 1966, Alhaji Yusuf Bayero ya koma gida Kano, inda aka nada shi Hakimin karamar hukuma Ajingi, inda ya kafa tarihin zama mutum na farko da ya rike sarautar.

Sai dai tsohon gwamnan Kano marigayi Abubakar Rimi ya sauke shi daga Hakimcin karamar hukumar ta Ajingi a shekarar 1981, daga bisani kuma marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ya sake maida mishi sarautar dan Ruwata amma hakimin Bichi, daga nan aka rika daga darajar sarautarsa zuwa Dan Isan Kano, Dan Buram da kuma Barde duk a lokacin da yake shugabantar Bichi.

A shekarar 1993 ne kuma Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayero, ya daga likkafar kanin nasa Yusuf Bayero zuwa saarautar Dan Iya, tare da maida shi zuwa hakimin Dawakin Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.