Najeriya-Kano

Coronavirus: An tsare shugaban karamar hukuma saboda karkatar da kayan tallafi

Gwamnan JIhar Kano Abdullahi Umar Ganduje, yayin kaddamar da shirin rabawa marasa karfi tallafin kayayyakin abinci, don rage musu radadin tasirin annobar coronavirus.
Gwamnan JIhar Kano Abdullahi Umar Ganduje, yayin kaddamar da shirin rabawa marasa karfi tallafin kayayyakin abinci, don rage musu radadin tasirin annobar coronavirus. Voice of Nigeria

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma sauraron korafe korafe ta jihar Kano, ta tsare shugaban karamar hukumar Kumbotso Alhaji Kabiru Ado Panshekara, bisa tuhumar da amfani da karfin kujerarsa wajen karkatar da tallafin kayan masarufin gwamnati na ragewa jama’a radadin dokar hana su fita saboda annobar coronavirus.

Talla

Shugaban hukumar yakar cin hancin da rashawar ta Kano Muhyi Magaji Rimingado ya tabbatar da kamen da suka yiwa Kabiru Ado Panshekara a yau asabar, kamar yadda jaridar Solacebase dake birnin na Kano ta tabbatar.

Muhuyi Magaji yace hujjoji sun bayyana yadda shugaban karamar hukumar ta Panshekara ya karkatar da kayayyakin abincin da aka mika masa don tallafawa marasa karfi, ta hanyar rabar dasu ga jami’an tsaron da suka hada da na ‘Yan Sanda, DSS da, jami’an kula da shige da fice wato Immigration a turance, sai kuma wasu jami’an hukumar Hisbah, abinda ya sabawa sashi na 22, da 23 da kuma 26 dake karkashin dokar 2008 da ta kafa hukumar sauraron korafe korafen al’umma da yakar cin hanci da Rashawar ta Kano.

Zuwa lokacin wallafa wannan labari babu karin bayani daga shugaban karamar hukumar ta Kumbotso ko kuma makusantansa dangane da matsayarsu kan tuhumar da ake masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.