Najeriya-Coronavirus

Gwamnan Bauchi ya kafa dokar hana fita a kananan hukumomi 3

Gwamnan JIhar Bauchi Sanata Bala Muhammad.
Gwamnan JIhar Bauchi Sanata Bala Muhammad. RFI Hausa / Shehu Saulawa

Gwamnan Bauchi Sanata Bala Muhammad ya kafa dokar hana fita a wasu kananan hukumomin jihar 3, da suka hada da Giyade, Zaki da kuma Katagum.

Talla

Gwamnan yace kafa dokar kullen ya zama dole, la’akari da yadda annobar coronavirus ke dada kaifi a jihar.

A yau Lahadi ne dai alkalumman ma’aikatar lafiyar Bauchin suka nuna cewar mutane 27 daga cikin karin 44 da suka kamu da cutar ta coronavirus a jihar daga garin Azare suka fito, dake karamar hukumar Katagum.

Dokar hana fitar kan kananan hukumomin uku za ta soma aiki ne daga karfe 6 na yammacin ranar Talata, 12 ga watan Mayu.

Zuwa lokacin wallafa wanna labari dai kamar yadda alkalumman hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya suka nuna, jumillar mutane 161 suka kamu da cutar coronavirus a Bauchi, daga cikinsu 6 sun warke, yayinda mutum 1 ya mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.