Coronavirus-Lagos

Rashin mutunta doka zai janyo sake haramtawa mutane fita a Legas - Sanwo-Olu

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, tare da mataimakinsa Obafemi Hamzat daga hadu, sai kuma kwamishinansa na lafiya Farfesa Akin Abayomi.
Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, tare da mataimakinsa Obafemi Hamzat daga hadu, sai kuma kwamishinansa na lafiya Farfesa Akin Abayomi. LASG

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu, ya gargadi al’ummar jihar da su rika bin dokokin kaurcewa cinkoso, ko kuma gwamnati ta sake kafa dokar hana fita don dakile yaduwar cutar coronavirus.

Talla

Sanwo-Olu yayi gargadin ne a lokacin da yake karin bayani kan halin da birnin Legas ke ciki dangane da yaki da annobar coronavirus.

Gwamnan ya koka kan yadda mutane da dama a jihar basa bin dokoki da sharuddan da gwamnati ta gindaya don dakile cutar COVID-19 a daidai lokacinda aka sakarwa jama’a mara don komawa hada-hadar yau da kullum, bayan shafe akalla makwanni 5 a kulle.

Rahotanni daga jihar ta Legas dai na cewa bayan sassauta dokar hana fitar da gwamnati tayi daga ranar 4 ga watan Mayu, an samu wurare da dama da mutane ke yin aro musayar takunkumi, ko kyallen rufe baki da hanci, musamman a yayinda ake bin layin shiga bankuna, gangancin da Gwamna Sanwo-Olu yace ba zai lamunta.

Sanwo-Olu ya kuma sha alwashin cigaba da katse hanzarin motoci, manya ko kanana, da suke kokarin yin fasakaurin mutane zuwa cikin jihar, inda yace motocin dakon kayayyakin bukata kawai aka yarjewa shiga Jihar.

Alkalumman hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya sun nuna cewa kashi 42.5 cikin 100 na yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya na Jihar Legas, adadin da ya kai dubu 1 da 764.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.