Najeriya-Amurka

'Yan Najeriya 160 sun koma gida bayan shafe makwanni makale a Amurka

Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja a Najeriya.
Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja a Najeriya. The Guardian

Gwamnatin Najeriya ta kwaso ‘yan kasar 160 da suka shafe makwanni makale a Amurka, biyo bayan rufe iyakoki da daukacin kasashe suka yi, don dakile yaduwar annobar coronavirus a yanzu ta addabi duniya.

Talla

Jirgin kasar Habasha na Ethiopian Airlines ne yayi jigilar ‘yan Najeriyar inda a yau Lahadi ya sauka a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake birnin Abuja.

Tun a makon jiya gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin soma kwaso daruruwan ‘yan kasar da suka makale a kasashen ketare zuwa gida.

Daga cikin jumillar ‘yan Najeriyar 160 da aka maida gida daga Amurka, 60 mata ne, 8 kananan yara, sai kuma maza 92.

Tuni dai jami’an lafiya a Najeriyar suka kwashi daukacin mutanen da suka sauka a filin jiragen saman na Abuja, zuwa inda za a killace su tsawon mako 2, domin tabbatar da cewar basa dauke da cutar coronavirus kafin basu damar shiga cikin al’umma.

Kafin jigilar ‘yan kasar daga Amurka a yau Lahadi, kwanaki biyu da suka gabata, hukumomin Najeriyar suka mayarda ‘yan kasar 253 zuwa gida a ranar Juma’a 8 ga watan Mayu, bayan shafe makwanni makale a Birtaniya, wadanda suma yanzu haka aka killace tsawon kwanaki 14, kafin shiga cikin al’umma, idan ya tabbata basa dauke da cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.