Najeriya-Madagascar

Coronavirus: Buhari ya bada umarnin karbar maganin Madagascar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. © Nigeria Presidency/Handout via REUTERS

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bada umarnin karbar maganin da kasar Madagascar ta samar ta warkar da cutar coronavirus da kuma bada rigakafin kamuwa da ita.

Talla

Sakataren gwamnatin Najeriyar Boss Mustapha ne ya sanar da umarnin na shugaba Buhari a yau Litinin, yayinda yake karin bayani kan halin da ake ciki a kasar dangane da yakin da ake da annobar coronavirus.

Gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar amfani da maganin ne, bayanda sakon kayan tsimin gargajiyar da aka hada shi da ganyen Tazargade mai suna ‘Covid-Organics’ ya isa kasar ta hannun Guinea Bissau a matsayin kyauta, bisa umarnin shugaban Madagascar Andry Rajoelina.

Tuni dai kasashen Afrika da dama suka nemi maganin na ‘Covid-Organics’ duk da cewa hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci da yi taka-tsantsan gami da gwaje-gwaje kafin soma amfani da maganin.

Alkalumman hukumomin lafiya a baya bayan nan sun nuna cewar Madagascar da ta samar da maganin cutar coronavirus na ‘Covid-Organics’ har yanzu na da jumillar mutane 193 ne da suka kamu da coronavirus, daga cikinsu kuma 101 sun warke, babu kuma wanda ya rasa ransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.