Najeriya-Jigawa

Fiye da rabin masu cutar coronavirus a Jigawa almajirai ne - Gwamnati

Wasu Almajirai a garin Maiduguri dake Najeriya. (An yi amfani da wannan hoto domin misali ne kawai)
Wasu Almajirai a garin Maiduguri dake Najeriya. (An yi amfani da wannan hoto domin misali ne kawai) Kolawole Adewale/Reuters

Gwamnatin Jigawa ta sanar da samun karin mutane 33 a jihar, da suka kamu da cutar coronavirus a Lahadin karshen makon nan.

Talla

Sai dai 16 daga cikin sabbin masu cutar coronar da aka gano a Jigawan almajirai ne da gwamnatin Kano ta maida su gida a baya bayan nan, yayinda sauran karin mutane 17 suka dauki cutar ta hanyar mu’amala da wadanda suka riga su kamuwa da ita.

Yayin karin bayani kan halin da ake ciki, shugaban kwamitin yakar cutar ta coronavirus a Jigawa Abba Zakari, yace jumillar mutanen da suka kamu da cutar a Jihar ya kai 116, kuma 60 daga cikinsu almajirai ne da aka maida su Jigawan daga Kano.

Abba Zakari ya kuma sanar da kafa dokar hana fita a daukacin karamar hukumar Ringim, wadda yace za ta soma aiki daga yau Litinin 11 ga watan Mayu, la’akari da cewa adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a yankin ya zarta na sauran sassan jihar.

Yanzu haka dai gwamnatin Jigawa na dakon sakamakon gwajin mutane 328 daga cikin jumillar 607 da suka mikawa kwararru a baya bayan nan, yayinda sakamakon mutane 279 ya fita, ciki har da mutane 60 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.