Gali Umar Na-Abba kan yadda suka koma Najeriya bayan makalewa a Turai

Sauti 03:19
Tsohon Kakakin majalisar wakilan Najeriya Alhaji Gali Umar Na-Abba.
Tsohon Kakakin majalisar wakilan Najeriya Alhaji Gali Umar Na-Abba. allAfrica.com

Gwamnatin Najeriya na ci gaba da kwaso ‘yan asalin kasar da suka makale a kasashen ketare, sakamakon dokokin da ke hana tafiye-tafiye tsakanin kasa da kasa.Daga cikin ‘yan Najeriyar da aka kwaso akwai wadanda aka kwaso daga Amurka, Birtaniya da kuma Dubai.Tsohon Kakakin majalisar wakilan Najeriya Alhaji Gali Umar Na'Abba, na daga cikin mutanen da aka kwaso daga Birtaniya amma kuma yanzu haka suke a killace, ya bayyana wa Muhammad Kabir Yusuf halin da aka dawo da su Najeriya.