Najeriya-Kano

Jumillar ma'aikatan lafiya 47 sun kamu da cutar coronavirus a Kano

Wani jami'in lafiya a Abuja babban birnin Najeriya, yayin yiwa wani mutum gwajin cutar corona a ranar 15 ga Afrilu, 2020.
Wani jami'in lafiya a Abuja babban birnin Najeriya, yayin yiwa wani mutum gwajin cutar corona a ranar 15 ga Afrilu, 2020. REUTERS/Afolabi Sotunde

Gwamnatin Jihar Kano dake Najeriya ta tabbatar da cewar ma’aikatan lafiya 47 suka harbu da cutar COVID-19 a Jihar, a aikin da suke wajen ceto rayukan jama’a.

Talla

Shugaban kwamitin yaki da cutar Dr Tijjani Hashim yace a kwanakin da suka gabata aka samu wannan adadi, amma ya zuwa yanzu babu wani sabon ma’aikacin da ya kamu da cutar.

Dr Hashim yace a kokarin da gwamnatin Jihar take wajen tunkarar matsalar, yanzu haka an horar da ma’aikatan lafiya sama da dubu 1,000 domin kare lafiyarsu.

Shugaban kwamitin yace an tabbatar da mutane 576 da suka kamu da cutar a Kano, yayin da 32 suka warke, 21 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.