Bakonmu a Yau

Kashi 50 na masu cutar coronavirus a Jigawa Almajirai ne

Sauti 04:03
Wasu almajirai a Najeriya (An yi amfani da wannan hoto domin misali kawai)
Wasu almajirai a Najeriya (An yi amfani da wannan hoto domin misali kawai) Reuters

Gwamnatin Jigawa dake Najeriya ta sanar da cewar yanzu haka Jihar ta samu mutane 116 da suka kamu da cutar coronavirus, kuma 60 daga cikin su almajirai ne da aka kai su Jihar daga Kano.Yayin zantawa da Bashir Ibrahim Idris, shugaban kwamitin yaki da cutar Dr Abba Zakari yace ya zuwa yanzu sun gwada mutane 607 a Jihar, kuma sun samu sakamakon mutane 279.