Najeriya

Lokaci yayi da zan janye daga siyasa - Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan bayan mika mulki ga shugaba Muhammadu Buhari, ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2015.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan bayan mika mulki ga shugaba Muhammadu Buhari, ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2015. REUTERS/Afolabi Sotunde TPX IMAGES OF THE DAY

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana aniyar sa ta janyewa daga harkokin siyasa domin mayar da hankali kan ayyukan jinkai.

Talla

Jonathan ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga taron ‘yayan Jam’iyyar sa ta PDP dake Jihar Bayelsa, inda yake cewa daukar matakin zai bashi damar mayar da hankali kan ayyukan da Gidauniyar sa keyi wanda zai shafi al’ummar kasar maimakon siyasa.

Tsohon shugaban ya shaidawa Yan Jam’iyar su cewar, kada gwuiwar su tayi sanyi idan basu gan shi wajen harkokin jam’iyyar ba, kuma wannan ya say a halrci bikin na karshen mako domin bayyana musu matsayin da ya dauka.

Jonathan yace aniyar sa itace janyewa daga harkokin siyasa domin tinkarar aikin jinkai kamar yadda wadanda ke bukatar hadin kai da shi suka bukata.

Tsohon shugaban yace bayan jagorancin Najeriya, lokaci yayi da zai mayar da hankalin sa ta wani fannin da jama’a zasu ci moriyar sa, wadda hakan zai baiwa jama’a a Jihar sa da Najeriya cin moriyar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.