Najeriya-Bauchi

Tsananin zafi ne ya haddasa mace-mace a Bauchi ba coronavirus ba - Gwamnati

Gwamnan JIhar Bauchi Sanata Bala Muhammad.
Gwamnan JIhar Bauchi Sanata Bala Muhammad. RFI Hausa / Shehu Saulawa

Gwamnatin Jihar Bauchi tace tsananin zafin rana ne ya haddasa mace-mace da dama da aka gani a garin Azare, ba cutar coronavirus ba kamar yadda wasu ke zargi.

Talla

Mataimakin gwamna, kuma shugaban kwamitin yaki da annobar coronavirus a jihar ta Bauchi Baba Tela ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a karshen mako.

Tela yace babu gaskiya cikin rahoton dake cewar akalla mutane 300 suka mutu cikin kwanaki 10 a garin Azare, cikin yanayin da ake kyautata zaton cewar annobar coronavirus ce ta halaka su.

Mataimakin gwamnan yace gaskiyar lamari shi ne mutane 150 kawai suka mutu, inda yace adadin mutane 300 ko sama da haka da wasu ke yadawa aringizo ne kawai aka yi, zalika tsananin zafi ne yayi sanadin rayukansu.

Sai dai bisa ga dukkanin alamu har yanzu akwai sauran kura, domin kuwa akwai wasu daga cikin al’ummar jihar ta Bauchi da basu gamsu da bayanan gwamatin ba, la’akari da cewar a baya bayan nan wani tsohon dan majalisar tarayya daga Jihar Ibrahim Muhammad Baba, ya rubuta wasika ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, inda ya bukaci daukar matakin gaggawa kan abinda ya kira barkewar annobar coronavirus da ta halaka mutane da dama a garin Azare, adadin da wasu ke yada cewar ya haura mutane 300 a kwanaki kalilan.

A Jihar Jigawa ma dai an samu mace-mace da dama cikin karamar hukumar Hadeja a baya bayan nan inda gwamman mutane suka mutu cikin kwanaki kalilan a yanayin da wasu ke zargin cewa annobar coronavirus ce ta halaka su.

Sai dai a yayin zantawa da manema labarai, tsohon mataimakin gwamnan Jihar ta Jigawa kuma Sanata mai wakiltar arewacin Jihar a zauren majalisar dattijai Ibrahim Hassan Hadeja, yace babu alaka tsakanin mace-macen da coronavirus, inda yace tsananin zafi, da yin azumi cikin yanayin zafin gami da wasu cutukan na daban ne suka yi sanadin yawaitar mace-macen a karamar hukumar ta Hadeja.

Sanatan ya kara da cewar adadin mutanen da suka mutu kuma bai kai 100 ba, kamar yadda ake yayatawa, domin kuwa binciken kwamitin da gwamnatin Jihar Jigawa ta kafa kan lamarin ya gano cewar mutane 46 ne suka rigamu gidan gaskiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI