Bakonmu a Yau

Yadda annobar coronavirus ta shafi tashohin jiragen ruwan Najeriya

Sauti 03:55
Muhammad Abba-Kura, Kontrolan Kwastam a tashar jiragen ruwa ta Apapa dake Legas a Najeriya.
Muhammad Abba-Kura, Kontrolan Kwastam a tashar jiragen ruwa ta Apapa dake Legas a Najeriya. RFI Hausa / AbdoulKareem Ibrahim Shikal

Coronavirus, annoba ce da ta shafi kusan kowace bangare ciki har da na tattalin arziki a duniya, a wasu kasashen kasashen kuma lamurra suka tsaya cak tsawon watanni biyu zuwa uku da suka gabata sakamakon wannan annoba.Sai dai a Najeriya, bangaren sufuri musamman na ruwa na daga cikin fannonin da gwamnatin kasar ta baiwa damar kasancewa a bude tsawon wannan lokaci.Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta Kontrolan Kwastam a tashar jiragen ruwan Apapa, Muhammad Abba-Kura, domin jin ko watakila wannan matsala ta shafi aikinsu da kuma kudaden shigar da suke samarwa Najeriya a tashar ta Apapa dake birnin Legas.