Najeriya

EFCC ta cafke wasu 'yan China bisa kokarin bata cin hancin naira miliyan 100

Wasu 'yan kasar China 2 da hukumar EFCC ta kama suna kokarin baiwa daya daga cikin shugabanninta cin hancin naira miliyan 100.
Wasu 'yan kasar China 2 da hukumar EFCC ta kama suna kokarin baiwa daya daga cikin shugabanninta cin hancin naira miliyan 100. RFI Hausa

Hukumar EFCC dake Najeriya ta sanar da damke wasu 'yan kasar China guda biyu Meng Kun da Xu Koi da ake zargin cewar sun yi kokarin baiwa shugaban hukumar reshen Sokoto cin hancin naira miliyan 100, domin kaucewa yin bincike kan zargibn badakalar hakar ma’adinai a Jihar Zamfara.

Talla

Mai Magana da yawun hukumar Dele Oyewale yace mutanen biyu sun bukaci kawar da wani bincike da Hukumar keyi ne kan wani kamfanin gini da ake kira China Zhonghao dake yiwa gwamnatin Zamfara kwangila tsakanin shekarar 2012 zuwa 2019.

Oyewale yace tuni ofishin su dake Sokoto ya kaddamar da bincike akan wasu ayyukan da kamfanin yayi na hanyar mota a garuruwan Gummi da Bukkuyum da anka da Nasarawa dake Jihar Zamfara, tare da aikin gina rijiyar birtsatsai masu amfani da hasken rana 168 a kananan hukumomi 14 dake Jihar.

EFCC tace binciken ya biyo bayan bayanan asiri da ya nuna almundahana da zamba cikin aminci da kuma halrta kudaden haramun da ake yiwa wasu jami’an gwamnatin Jihar Zamfara wanda aka ce tuni kamfanin ya karbi kudin da ay kai naira biliyan 41 amma kuma aka karkata wasu naira biliyan 16 da hukumar ta gano wajen ‘yan canji.

Ganin cewar bincike ya ritsa da su, inji hukumar EFCC, ya sa ‘Yan kasar china suka bukaci baiwa shugaban shiyar Sokoto Abdullahi Lawai cin hanci naira miliyan 100 domin kashe maganar, amma kuma hakar su bata cimma ruwa ba.

Oyewale yace Lawal ya karbi naira miliyan 50 daga hannun wakilan kamfanin biyu Meng Wei Kun da Xu Kuoi a ofishin su dake hanyar zuwa tashar jiragen saman Sokoto a matsayin kashin farko, abinda ya sa aka damke su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.