Najeriya-Kano

Gwamnatin Kano ta tsawaita wa'adin dokar kulle

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Solacebase

Gwamnatin Kano ta kara wa’adin dokar killace mutane a gida da tsawon mako 1, in banda dai-daikun ranakun da ta baiwa jama’a damar fita.

Talla

Cikin sanarwar da gwamnatin Kanon ta fitar ta hannun kwamishinan yada labaranta Malam Muhammad Garba, tace daukar matakin ya biyo bayan tattaunawar gwamnati da kwararru da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya.

Sanawar ta bukaci al’ummar Kano da su kara hakuri tare bin dokokin kiyaye tsafta, kauracewa cinkoso da kuma sanya takunkumin rufe baki da hanci a lokacin fita daga gida.

Makwanni biyu da suka gabata ne dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin killace daukacin jihar Kano ba shiga ba fita, da kuma kafa dokar hana jama’a fita, domin dakile cutar coronavirus, da tun a waccan hukumomin lafiya suka ce tayi karfi wajen yaduwa.

Bayaga umarnin killace jihar, Buhari ya kuma tura tawagar kwararru don taimakawa ma’aikatar lafiyar birnin da gudanar da bincike kan mace-macen mutane da dama da aka samu cikin kwanaki kalilan da wasu ke alakantawa da barkewar annobar ta coronavirus.

A halin yanzu dai jumillar mutane 666 gwaji ya tabbatar da cewa suna dauke da cutar coronavirus a Kano, abinda ya sanya ta zama jihat ta biyu a Najeriya bayan Legas, inda annobar ta karfi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.