Coronavirus

Najeriya: Yawan wadanda suka warke daga cutar COVID-19 ya haura 900

Wani ma'aikacin lafiya, yayin tantance gwaje-gwajen da aka yiwa jama'a kan cutar coronavirus.
Wani ma'aikacin lafiya, yayin tantance gwaje-gwajen da aka yiwa jama'a kan cutar coronavirus. Jane Barlow/Pool/AFP

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta sanar da samun karin mutane 242 da suka kamu da cutar coronavirus, abinda ya sanya jumillar adadin masu dauke da cutar a Najeriyar kaiwa dubu 4 da 641.

Talla

Sabbin alkalumman na zuwa ne bayanda shugaban kasar Muhd Buhari, ya bada umarnin karbar maganin ‘Covid-Organics’ da Madagascar ta samar don warkar da cutar ta COVID-19 da kuma rigakafinta.

Alkalumman da hukumar ta NCDC ta fitar a daren jiya Litinin, sun nuna cewar an samu karin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a jihohin 14, da suka hada da Legas, inda aka gano sabbin mutane 88, 64 a Kano, 49 a Katsina, Kaduna 13, Ogun 9, Gombe 6, Adamawa mutane 4, sai Abuja mai mutune 3.

Sauran jihohin da aka samu karin masu dauke da cutar ta coronavirus, su ne Ondo, Oyo, Rivers, Bauchi Borno da kuma Zamfara, dukkaninsu mutum guda-guda.

A wannan karon dai mutane 10 annobar ta coronavirus ta halaka cikin rana guda a Najeriyar sabanin 17 a ranar Lahadi inda a yanzu jumillar mutane 150 kenan suka mutu, yayinda wasu 902 suka warke daga cikin dubu 4 da 641 da suka kamu.

Jihohi biyar dake kan gaba wajen yawan masu cutar ta coronavirus a Najeriyar sun hada da Legas mai mutane dubu 1, da 933, sai Kano mai 666, Abuja 359, Sai Katsina mai jumillar mutane 205, yayinda Borno ke da 186.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.