Najeriya-Coronavirus

Bata-gari na saida kyallen rufe fuskar da aka tsinto daga shara - Gwamnati

Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Najeriya, kuma shugaban kwamitin yaki da annobar coronavirus a kasar.
Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Najeriya, kuma shugaban kwamitin yaki da annobar coronavirus a kasar. © Nigeria Presidency

Gwamnatin Najeriya ta hannun kwamitinta na yakar annobar coronavirus, ta koka kan yadda wasu bata-gari ke saidawa ‘yan kasar kyallaye ko takunkuman rufe baki da hanci da aka yasar a shara bayan wanke shi.

Talla

Yayinda yake bayyana sabuwar hanyar ta bata-garin ke cutar da jama’a, sakataren gwamnatin kasar kuma shugaban kwamitin kasar na yaki da cutar coronavirus, Boss Mustapha, yayi gargadin cewa, lamarin zai kara munin yanayin da annobar ta jefa jama’a ciki, musamman ta fuskar kara karfin yaduwarta.

Tun bayan bullar annobar coronavirus a Najeriya, kyallaye ko takunkuman rufe baki da hanci suka kara daraja inda aka kara musu kudi, daga bisani kuma farashinsu ya sake hauhawa saboda rawar da yake takawa wajen baiwa mutane kariya daga shaka ko fitar da kwayoyin cutar ta coronavirus.

Yayin ganawa da manema labarai a Abuja, sakataren gwamnatin Najeriya Boss Mustapha ya kuma bukaci gwamnatocin jihohin arewacin Najeriya da su dakatar da maida almajirai zuwa garuruwansu na asali da kawo yanzu suka shafe makwanni suna yi tun bayan karfin da annobar coronavirus tayi a Najeriya.

A gefe guda kuma, Ministan Lafiyar Najeriya Dakta Osagie Ehanire da shi me ke cikin kwamitin yakar annobar coronavirus na kasar, ya sanar da tura tawagogin kwararru zuwa jihohin Jigawa, Kano, Katsina, Bauchi, da kuma Sokoto, domin gudanar da bincike kan musabbabin mace-macen da aka samu da dama a jihohin cikin kwanaki kalilan, wadanda wasu ke alakantawa da barkewar annobar coronavirus ko COVID-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.