Matsayin masana kan tuhumar shugaban bankin Afrika da laifin fifita Najeriya da 'yan Najeriyar

Sauti 03:35
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da shugaban Bankin raya kasashen Afrika AFDB, Akinwumi Adeshina.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da shugaban Bankin raya kasashen Afrika AFDB, Akinwumi Adeshina. RFI Hausa / Bashir

Wasu ma’aikatan Bankin Raya Afirka sun bukaci kafa kwamitin bincike mai zaman kansa daga wajen bankin, domin gudanar da bincike kan korafe korafe 15 da suka yi akan shugaban bankin Akinwumi Adeshin,a na nuna san kai da fifita Najeriya da ‘Yan Najeriya wajen gudanar da harkokin bankin.Mutanen sun yi watsi da rahoton wanke Adeshina da shugabannnin gudanarwar bankin Afrikan suka gabatar, bayan binciken da suka yi.Wannan na zuwa ne bayan Adeshina ya samu goyan bayan kasashe da dama da kungiyar kasashen Afirka ta Yamma da ta AU domin sake takara.Bashir Ibrahim Idris ya zanta da Dr Dauda Muhammed Kontagora masanin tattalin arziki a Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.