Saudiya za ta maida 'yan Najeriya sama da dubu 11 gida
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Saudi Arabia ta sanar da shirinta na tasa keyar ‘yan Najeriya sama da 11,000 zuwa gida saboda yadda suka makale a kasar sakamakon annobar COVID-19.
Rahotanni daga Saudi Arabia sun ce tuni hukumomin kasar suka rubutawa ofishin Jakadancin Najeiya wasika dangane da matakin da suke shirin dauka na kwashe yan Najeriya 11,600 zuwa gida.
Majiyar labarin ta shaidawa Jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriya cewar, wasu daga cikin wadannan mutane sun hada da wadanda suka je Umrah amma suka kasa komawa gida saboda dokar hana zirga zirga da kuma wadanda suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba.
Saudi Arabia da ta samu mutum na farko dake dauke da coronavirus a ranar 2 ga watan Maris, ta sanya dokar hana zirga zirga a ciki da wajen kasar, kafin daga bisani ta fadada shi zuwa kasashen Turai da wasu Karin kasashe 12, a ranar 12 ga watan Maris.
Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya tabbatar da labarin, inda yake cewa kalubalen dake gaban gwamnatin sun yi yawa, shi yasa basu iya kaiwa ‘yan Najeriyar dake kasar ta Saudiya dauki ba.
Ya zuwa yanzu dai Najeriya ta debo yan kasarta da suka makale a Dubai da London da kuma Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu