Najeriya-Nijar

'Yan bindiga sun tilastawa mutane dubu 42 tserewa daga iyakokin Najeriya da Nijar - MDD

Wasu mata 'yan Najeriya daga cikin dubban 'yan kasar da matsalar tsaro ta raba da muhallansu, inda suka tsere zuwa Ngouboua daje Chadi.
Wasu mata 'yan Najeriya daga cikin dubban 'yan kasar da matsalar tsaro ta raba da muhallansu, inda suka tsere zuwa Ngouboua daje Chadi. REUTERS/Emmanuel Braun

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla fararen hula dubu 42 ne suka tserewa hare-haren ‘yan bindiga daga kauyukan kan iyakar kasashen Najeriya da Nijar.

Talla

Cikin bayanan da hukumar ta wallafa a shafinta, ta ce adadin kari ne kan wasu mutanen dubu 23 da karancin tsaro ya tilastawa tserewa daga yankunansu akan iyakar Najeriya cikin watan jiya, yayinda wasu karin fararen hula dubu 19 a Jamhuriyyar Nijar suka rasa matsugunansu wanda ke da nasaba da karancin tsaron da garuruwan kan iyaka ke fuskanta a kasashen biyu.

A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce sakamakon tsoro da gujewa matsalar rashin tsaro a kan iyakokin kasar Nijar, ya tilastawa wasu al'ummar kasar dubu 19 zama yan gudun hijira a cikin kasarsu ta asali.

Hukumar ta ce jihohin Najeriya da a halin yanzu ke fama da rikice rikice sun hada da sokoto, da Katsina da Kuma Zamfara

Rahoton yace hari mafi muni a baya bayan nan shi ne na ranar 18 ga watan Afrilun da ya gabata inda akalla mutane 47 suka rasa rayuwarsu a jihar katsina

Yankin arewacin Najeriya dai yayi kaurin suna wajen fama da rikice-rikicen kabilanci musamman rikici a kan filaye da ruwa, sai kuma a baya bayan satar mutane da hare-haren ‘yan bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.