Najeriya-Coronavirus

Adadin wadanda suka warke daga cutar corona a Najeriya ya haura dubu 1

Wata mata a kasuwar Dutse Alhaji dake Abuja, babban birnin Najeriya. 2/5/2020.
Wata mata a kasuwar Dutse Alhaji dake Abuja, babban birnin Najeriya. 2/5/2020. REUTERS/Afolabi Sotunde

Yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai dubu 4,971, bayan da a daren jiya laraba hukumar yaki da yaduwar cutuka ta kasar NCDC ta sanar da samun karin mutane 184 da suka kamu da cutar a rana guda.

Talla

Hukumar ta NCDC tace an samu karin mutanen ne a jihohin Najeriya 22 da suka hada da Legas, inda aka samu karin mutane 51, sai jigawa mai 23, mutane 16 a Bauchi, sai Katsina mai mutane 16, yayinda a Kano aka samu karin 14.

A sauran jihohin, Rivers da Birnin Abuja na da mutane 10-10, sai 9 a Kwara, yayinda Delta da Kaduna ke da 5-5, Sokoto da Oyo nada mutum 4-4, yayinda Kebbi, Nasarawa da Osun ke da mutane 3 kowannensu. Ondo na da mutane 2 da suka kamu, sai kuma jihohin Ebonyi, Edo, Enugu, Anambra, Filato da kuma Niger dukkaninsu da mutane 1-1.

Wani batu dake daukar hankali a sakon hukumar yaki da yaduwar cutukan ta Najeriya shi ne karuwar adadin wanda suka warke da cutar ta coronavirus, adadin da a yanzu ya kai dubu 1 da 70, yayinda jumillar yawan wadanda annobar ta kashe ya kai 164, bayan samun karin mutane 6 da annobar ta kashe jiya laraba a Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.