Matsayin kungiyar Amnesty kan matakin gwamnonin arewacin Najeriya na maida almajirai zuwa jihohinsu

Sauti 03:29
Wasu Almajirai a lokacin da suke bara a saman tituna a yankin arewacin Najeriya.
Wasu Almajirai a lokacin da suke bara a saman tituna a yankin arewacin Najeriya. Arewa aid

Yayinda ake cigaba da kwashe almajirai zuwa Jihohinsu na asali a Yankin Arewacin Najeriya, wasu kungiyoyin fararen hula sun koka kan yadda ake gudanar da aikin da kuma yadda ake cin zarafin yaran.Wannan na zuwa ne bayanda itama gwamnatin Najeriya ta hannun sakatarenta kuma shugaban kwamitin gaggawa na yakar annobar coronavirus Boss Mustapha ta bukaci dakatar da aikin saboda hadarin dake tattare da shi.A farkon watan Mayun nan, Gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa’i ya bayyana kawo karshen almajiranci a jiharsa, inda yace tuni ya samu nasarar mayrda almajirai dubu 30,000 zuwa jihohinsu na asali.Dangane da wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Manajan hulda da jama’a na kungiyar Amnesty International Malam Isa Sanusi.