Najeriya

Mutane kusan 500 sun mutu cikin makwanni 3 a Yobe

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni. BUNIMEDIA

Kwamitin yaki da annobar coronavirus da gwamnatin Yobe ta kafa, yace mutane 471 ne suka mutu a jihar cikin makwanni uku da suka gabata.

Talla

Kwamishinan lafiyar jihar ta Yobe Dakta Muhammad Lawan Gana, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kwamitin yakar annobar ta coronavirus, yace mafi akasarin mutanen da suka rasu, dattijai ne, da suka fito daga Nguru, Gashua, da kuma Damaturu.

Wasu daga cikin al’ummar jihar ta Yobe dai na fargabar cewa akwai alaka tsakanin mace-macen da cutar coronavirus, kamar yadda aka yi zaton haka a jihohin Jigawa, Kano da kuma Bauchi.

Sai dai gwamnatin Yobe musanta rade-radin, tara bayyana zazzabin malaria, tsananin zafi, da kuma cutar hawan jinni a matsayin dalilan da suka haddasa mace-macen, amma ba coronavirus ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.