Najeriya na nazarin karbar bashin euro biliyan 1 kan noman zamani
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Najeriya za ta ciyo bashin kudi har kusan Euro biliyan guda, a yunkurinta na farfado da noman zamani, sakamakon yadda aikace-aikacen ‘yan ta’adda dana masu garkuwa da mutane a yankunan Arewa maso yammaci da Arewa maso gabashin kasar ya tilstawa manoma barin gonakansu.
Bayaga matsalolin tsaron da suka durkusar da ayyukan noman a Najeriya, annobar COVID-19 da a baya bayan nan ta addabi duniya, ta kara janyowa fannin noman koma baya, bayan tilastawa mutane zaman gida.
Akan wannan batu, wakilinmu a Abuja Muhammad Kabir Yusuf ya hada rahoto.
Najeriya na nazarin karbar bashin euro biliyan 1 kan noman zamani
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu