Najeriya-Jigawa

Yawan masu cutar coronavirus a Jigawa ka iya kaiwa dubu 20 - Badaru

Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar.
Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar. RFI Hausa/Abubakar Isa Dandago

Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, yayi gargadin cewar adadin wadanda ka iya kamuwa da cutar coronavirus ko COVID-19 a Jihar zai iya kaiwa dubu 20, ganin yadda a halin yanzu cutar ke yaduwa cikin gaggawa a Jigawan.

Talla

Yayin ganawa da manema labarai a Dutse, ranar larabar nan da ta gabata, Gwamnan Jigawan yace a yanzu haka annobar ta coronavirus ta yadu zuwa kananan hukumomi guda 8 daga cikin jumillar 27 dake Jihar.

Sai dai gwamnan yace idan aka yi sa a annobar bata zarta matakin kashi 14 cikin 100 na saurin yaduwar da take a jihar ba, adadin wadanda ake hasashen za su kamu da cutar a jihar ka iya tsayawa a dubu 8.

Rahoton da hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta wallafa a daren ranar laraba 13 ga watan Mayu, ya nuna cewar daga cikin karin mutane 184 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar, Jigawa ce jiha ta biyu bayan Legas mai yawan sabbin wadanda suka kamun da mutane 23.

A mataki na kasa baki daya kuwa, Jigawa na da jumillar mutane 141 da suka kamu da cutar, abinda ya sanya ta zama ta bakwai a jerin jihohin Najeriya 34 da annobar at COVID-19 ta bulla cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.