Najeriya-Coronavirus

Atiku ya bukaci Buhari ya zaftare kasafin abincinsa dana tafiye-tafiye

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya.
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

Tsohon mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo, dasu zabtare kasafin kudin da aka amince musu na abincin da za su ci, da kuma kudin da za su kashe wajen tafiye-tafiye saboda illar da annobar COVID-19 ta yiwa kudaden shigar da kasar ke samu.

Talla

A budaddiyar wasikar da ya rubutawa shugabannin tare da shugabannin Majalisun dokoki, Atiku yace ganin yadda farashin mai ya fadi da kuma daina samun kudaden shiga ta wasu hanyoyin da aka saba, rage kasafin kudin da gwamnati tayi na kasa da kashi 6, wato daga naira triliyan 10,594 zuwa triliyan 10,523 ya gaza.

Atiku yace kuskure ne Majalisar dokokin kasar tace za ta kashe naira biliyan 27 wajen yiwa gininta kwalliya a halin da ake ciki, kamar yadda ya bukaci zabtare biliyoyin nairorin da aka ware wajen kashewa shugaban kasa da mataimakinsa da kuma shugabannin majalisun.

Tsohon Mataimakin shugaban kasar, ya kuma bukaci soke shirin sayawa shugaban kasa da mataimakinsa sabbin motoci na kawa tare da wasu masu rike da mukaman gwamnatin, kana kuma ya bukaci sayar da jiragen fadar shugaban kasa akalla 8 zuwa 9 da rage kasafin kudin Najeriya na wannan shekara da akalla kashi 25.

Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasar yayi watsi da duk wani shiri da zai taba albashin ma’aikata wadanda ya bayyana a matsayin masu sadaukar da rayukansu, yayinda ya bada shawarar zabtare albashin masu rike da mukaman siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.