Bakonmu a Yau

Dr Isa Abdullahi kan sabon rahoton da yace kashi 40 na al'ummar Najeriya matalauta ne

Sauti 03:38
Bincike ya nuna kashi 40 na al'ummar Najeriya na rayuwa cikin kangin talauci.
Bincike ya nuna kashi 40 na al'ummar Najeriya na rayuwa cikin kangin talauci. Akintunde Akinleye/Reuters

Hukumar Kididdiga dake Najeriya ta bayyana mazauna Jihohin Sokoto da Taraba da Jigawa a matsayin wadanda suka fi fama da talauci, inda take cewa ko wadanne mutane 9 daga cikin 10 na fama da tsananin talauci a cikin su.Rahotan da hukumar yace daga cikin Yan kasar kusan miliyan 207, kusan miliyan 83 wato sama da kashi 40 matalauta ne, wadanda ke rayuwa a kasa da naira 377 kowacce rana, ko kuma naira 11,453 Kowanne wata.Dangane da wannan rahoto Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Isa Abdullahi, na Jami’ar Kashere, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.