Najeriya-Coronavirus

Najeriya ta kafa dokar tilastawa mutane saka takunkumin rufe fuska

Wasu 'yan Najeriya a birnin Abuja, bayan sassauta dokar hana zirga-zirga a ranar litinin. 4/5/2020.
Wasu 'yan Najeriya a birnin Abuja, bayan sassauta dokar hana zirga-zirga a ranar litinin. 4/5/2020. REUTERS/Afolabi Sotunde

Gwamnatin Najeriya tace yin amfani da kyallen dake rufe baki da hanci a cikin kasar ya zama dole ga dukkan Yan kasa domin kare kai daga annobar coronavirus.

Talla

Shugaban kwamitin yaki da cutar kuma Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya sanar da haka, inda yake cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan dokar saboda haka ya zama wajibi ga jami’an tsaro su tabbatar da aiwatar da ita.

Mustapha ya bukaci gwamnonin jihohin Najeriya 36 da su tabbatar da aiwatar da dokar a Jihohin su domin ganin anyi nasarar dakile wannan annoba.

Sakataren gwamnati yayi gargadi kan masu daukar kyallen rufe fuskar a shara suna sayarwa mutane wanda yace laifi ne babba.

Tuni wasu gwamnatocin jihohi suka aiwatar da irin wannan doka a Jihohin su, cikin su harda Lagos da Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.