Najeriya-Tattalin arziki

Sokoto, Jigawa da Taraba ke kan gaba wajen fama da talauci a Najeriya - Rahoto

Bincike ya nuna kashi 40 na al'ummar Najeriya na rayuwa cikin kangin talauci.
Bincike ya nuna kashi 40 na al'ummar Najeriya na rayuwa cikin kangin talauci. Akintunde Akinleye/Reuters

Hukumar kididdiga dake Najeriya ta bayyana mazauna Jihohin Sokoto da Taraba da Jigawa a matsayin wadanda suka fi fama da talauci, inda take cewa ko wadanne mutane 9 daga cikin 10 na fama da tsananin talauci a cikinsu.

Talla

Rahoton da hukumar kula da kididdigar Najeriya ta gabatar ya nuna cewar daga cikin ‘yan kasar kusan miliyan 207, kusan miliyan 83 wato sama da kashi 40 matalauta ne, wanda shi ne adadi mafi muni ga duk wata kasa a duniya, abinda ke nuna cewar ya zama dole sai hukumomin kasar sun tashi tsaye wajen fitar da akalla mutane miliyan 17 daga talauci kafin Najeriya ta sauya sunanta daga cibiyar talauci.

Alkaluman dake nuna talaucin sun hada da mutanen dake samun kasa da naira 377 kowacce rana, ko kuma naira dubu 11,453 kowanne wata wadanda za’ayi amfani dasu wajen sayen abinci da sutura da kula da lafiya da samun ilimi, wutar lantarki da sauran kayan more rayuwa.

Jihohin Lagos da Delta da Osun da Ogun da Oyo da kuma Edo ke sahun gaba, wajen samun rayuwa mai inganci, yayinda alkalumman hukumar suka ce Jihar Sokoto ke karshe a mizanin nata sai Taraba da Jigawa da Ebonyi da Adamawa da Zamfara da kuma Yobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.