MDD za ta kashe dala miliyan 22 a Najeriya don yakar coronavirus
Wallafawa ranar:
Gidauniyar taimakawa Najeriya wajen shawo kan annobar COVID-19 da Majalisar dinkin Duniya ke sanya ido akai ta amince da shirin kashe dala miliyan 22 domin sayan kayayyakin kula da lafiya domin amfani dasu a cikin kasar.
Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya dake jagorancin gidauniyar Edward Kallon, yace sun amince da shirin kashi Dala miliyan 12 domin sayo kayayyakin da jami’an kula da lafiya ke sanyawa wajen gudanar da ayyukansu da ake kira PPE, yayinda suka amince da shirin kashe dala miliyan 10 wajen sayo kayayyakin da ma’aikatan lafiya ke aiki dasu a cibiyoyin gwaji.
Ita dai wannan gidauniyar tana da wakilai da dama cikinsu harda wakilin hukumar yaki da cutuka ta Najeriya da ministocin lafiya da na jinkai, da babban jami’in yaki da cutar Dakta Sani Aliyu, da wakilan kasashen Turai da ECOWAS.
Daga cikin wadanda suka bada gudumawa a asusun harda manyan attajiran Najeriya da Bankuna da kuma Kungiyar kasashen Turai da ta bada Euro miliyan 50.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu