Najeriya-Madagascar

Sakon Madagascar na maganin coronavirus ya isa Najeriya

Maganin Covid-Organics da kasar Madagascar ta samar mai warkar da coronavirus da kuma bada rigakafin kamuwa da cutar.
Maganin Covid-Organics da kasar Madagascar ta samar mai warkar da coronavirus da kuma bada rigakafin kamuwa da cutar. REUTERS/Gertruud Van Ettinger

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya karbi sakon maganin warkarwa da kuma rigakafin cutar coronavirus, da kasar Madagascar ta samar.

Talla

Buhari ya amshi sakon shatara ta arzikin na maganin ‘Covid-Organics da Madagascar ta aika zuwa Najeriya ne ta hannun shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo, wanda a yau asabar suka gana a Abuja, babban birnin Najeriya.

Cikin sakon da ya aike ta hannun Bashir Ahmad, mataimakinsa kan kafafen sadarwa na zamani, shugaba Buhari yace kamar yadda yayi alkawari a baya, kwararru daga fannin kimiyyar zamani da kuma gargajiya a karkashin jagorancin hukumar tantance ingancin abinci ta magunguna ta Najeriya NAFDAC, za su gudanar da karin bincike kan maganin na ‘Covid-Organics’ kafin soma amfani da shi kan masu cutar coronavirus a kasar.

Tuni dai wasu kasashen Afrika suka karbi maganin na 'Covid-Organics' ciki harda Nijar da kuma Tanzania.

Kawo yanzu dai kasar Madagascar da ta samar da maganin daga ganyen 'Artemisia' na da adadin mutane 238 da suka kamu da cutar coronavirus, daga cikinsu kuma 112 sun warke, zalika babu wanda ya rasa ransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.