Najeriya-Coronavirus

Yawan wadanda cutar COVID-19 ta kama a Najeriya ya kai 5,445

Wani mara lafiya a garin Maiduguri, yayin yi masa gwajin cutar coronavirus.
Wani mara lafiya a garin Maiduguri, yayin yi masa gwajin cutar coronavirus. Audu Marte/AFP/Getty

Hukumar yaki da cututtuka a Najeriya tace an samu Karin mutane 288 da suka harbu da cutar coronavirus a cikin sa’oi 24 da suka gabata, abinda ya kawo adadin mutanen da suka kamu a kasar zuwa 5,445, yayin da 1,320 sun warke, kana 171 sun mutu.

Talla

A Jihar Lagos kawai an samu jumillar mutane 2,278 da suka kamu da wannan cuta, sai Kano mai mutane 761, Abuja na da 386, sai Katsina mai mutane 239, sai Bauchi mai mutane 210, sai Barno mai mutane 204, sai Jigawa mai 191, sai Ogun mai mutane 145.

Sauran sun hada da Kaduna mai mutane 134, sai Gombe mai mutane 124, sannan Sokoto mai mutane 112.

Alkalumman hukumar yaki da yaduwar cutukan Najeriyar tace an samu karin mutane 288 a jiya Juma’a ne a jihohin Najeriya 15, inda a Legas aka gano sabbin mutane 179 da suka kamu, Kaduna na da 20, sai kastina da Jigawa masu 15-15, Borno karin mutane 13 ta samu, sai Ogun mai mutane 11, yayinda Kano ke da mutane 8.

A Abuja babban birnin Najeriya, an samu karin mutane 7 da suka kamu, sai Niger da Ekiti 4-4, Oyo, Delta da Bauchi mutane 3 kowannensu, sai Kwara mai mutum 2, da Edo mai mutum 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.