Najeriya-Coronavirus

Kusan mutane 1,500 sun warke daga coronavirus a Najeriya

Daya daga cikin masu aikin sa kai a Najeriya, dake aikin rabawa marasa karfi kayan abinci, yayin zaman gidan dole da annobar coronavirus ta janyo a birnin Legas dake Najeriya. 9/4/2020.
Daya daga cikin masu aikin sa kai a Najeriya, dake aikin rabawa marasa karfi kayan abinci, yayin zaman gidan dole da annobar coronavirus ta janyo a birnin Legas dake Najeriya. 9/4/2020. REUTERS/Temilade AdelajaReuters

Hukumomin Najeriya sun ce an samu karin mutane 176 da suka harbu da cutar coronavirus a cikin sa’oi 24 da suka gabata, abinda ya kawo adadin jama’ar kasar da suka harbu zuwa 5,621, kuma 176 sun mutu, yayinda 1,472 suka warke.

Talla

Daga cikin sabbin mutanen da suka kamu da cutar ta coronavirus, 95 sun fito daga Lagos, 31 a Oyo, sai kuma Abuja, inda aka samu karin mutane 11.

Sauran jihohin sun hada da Borno da Niger masu karin mutane 8-8, sai Jigawa mutane 6, a Kaduna kuma mutane 4. Jihar Anambra ke biye bayan samun karin 3, sai jihohin Nasarawa, Rivers, da Bauchi, yayinda Zamfara da Benue ke da mutum guda-guda.

Jihar Lagos ke sahun gaba wajen yawan mutanen da suka harbu da cutar a jumlace, inda take da 2,373, sai Kano mai 761, sai Abuja mai mutane 397, Katsina na da 239, Borno da Bauchi na da 212 kowacce, sai Jigawa mai 197.

Sauran sun hada da Kaduna mai mutane 138, Gombe 124, Sokoto 112.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.