Najeriya-Coronavirus

PDP ta baiwa gwamnatin Buhari wa'adin kwanaki 2 ta bayyana inda likitocin China suke

Tawagar likitocin kasar China da suka isa Najeriya don taimakawa kasar yaki da annobar coronavirus.
Tawagar likitocin kasar China da suka isa Najeriya don taimakawa kasar yaki da annobar coronavirus. YouTube

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta baiwa gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari wa’adin kwanaki biyu, da ta yi bayani kan tawagar likitocin da China da isa kasar tun cikin watan Afrilu da ya gabata, domin taimakawa Najeriyar wajen yakar annobar coronavirus.

Talla

Ranar 8 ga watan Afrilu tawagar likitocin ta China ta sauka a Najeriya, wadanda suka samu tarbar manyan jami’an kasar ciki harda ministan lafiya Osgie Ehanire, daga bisani gwamnati ta sanar da killace jami’an lafiyar na China inda za su shafe makawanni 2, domin tabbatar da cewa basa dauke da cutar coronavirus.

Tun daga waccan lokacin ne kuma ba a sake jin duriyar tawagar likitocin ba, duk da cewar sun kammala kwanaki 14 a killace.

Rashin sanin halin da ake ciki ne ya sanya jam’iyyar PDP a sakon da ta wallafa a shafinta na twitter baiwa gwamnatin Najeriya wa’adin kwanaki biyun da ta bayyana inda likitocin na China suke, inda kuma ta bayyana mamaki kan ikirarin ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire na cewar bashi da masaniyar inda jami’an lafiyar na China suke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.